Labaran Kannywood
Hafsat Shehu Matar marigayi kuma Jarumi a Kannywood Ahmad S Nuhu ta bayyana halin data shiga tun bayan rasuwar sa

Tsohuwar matar fitaccen Jarumin Masana’antar Kannywood Ahmad S. Nuhu wanda yake dan uwa ga Jarumi Ali Nuhu, ta bayyana mawuyacin halin da ta fada bayan rasuwarsa.
Matar Tsohon Jarumin mai suna Hafsat Shehu ta bayyana haka ne a wata hira da BBC Hausa a yayin da tauraron yake cika shekara 15 da rasuwa.
Tauraron ya rasu ne ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2007 sakamakon hatsarin mota a garin Azare na jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Kamar yadda ta fadi cewa: Ahmad Nuhu mutum ne da yake ganin mutunci da darajar mata.
Ga bidiyon nan domin kuji cikekkiyar shirar da BBC Hausa tayi da ita.