Advertising
Advertising
Labarai

Wata ‘yar gudun shijira a jihar Borno ta kashe kan ta bayan da wani ma’aikaci ya yi mata fyade

Wata 'yar gudun shijira a jihar Borno ta kashe kan ta bayan da wani ma'aikaci ya yi mata fyade

Har yanzu dai matsalar fyade tan akara tsamari a Nageriya musamman Arewacin kasar wanda a yanzu muka sami labarin an yiwa wata ‘yar gudun hijira fyade, wanda hakan yayi sanadiyyar ta kashe kan ta.

Advertising

A jihar Borno Arewa maso gabashin Nageriya wata ‘yar gudun hijira wanda take neman abin da zai rufa mata asiri ta hanyar yin aikuka a gidajen mutane, ta kashe kan ta bayan da wani ma’aikacin agaji ya keta mata haddi.

Lamarin ya faru ne a Badalance bayan nan ne matar ta cakawa kan ta wuka daga nan kuma tace ga garin ku nan ta mutu.

A yanzu haka jami’an tsaro sun kama mutumin da ake zargin shi ya aikatawa matar fyaden wanda har yayi sanadiyyar ta rasa ran ta, amma mutumin ya bayyanawa manema labarai cewa.

Advertising

Ba ni na mata fyade ba sannan kuma ba ni na kashe ta ba dalilin da yasa ake ganin kamar ni na kashe ta, tana zuwa inda nake ne shi yasa kawayan ta suke kiran ta da karuwa.

To abin ya yi mata zafi sannan kuma babu wani abu da zatayi wanda zai fidda ta daga zargin da kawayan nata suke mata, shi yasa ta aikatawa kan ta haka.

Sannan dama Aisha tana da zafin rai matuka wanda zata iya aikatawa kan nata haka ko da abin bai kai ya kawo ba.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button