Advertising
Advertising
Labarai

Maikatan Lafiya na shirin maka Sheikh Abdalla Gadon kaya a kotu in be janye kalaman sa na suna zina a asibitoci ba.

Wannan Shehin malamin nan mai tsage gaskiya komai dacin ta kan alamuran da ke faruwa a cikin al’umma wanda sau da dama irin wannan fadar gaskiya tasa kan jamasa tsangwama daga ba’arin da ya magantu a Kansu a wannan karon ya tabo ma’aikatan asibiti inda ya bayyana wasu abubuwa da yace suna faruwa a asibitocin mu na Allah wadai.

Advertising

Da dadewa malamin yayi lakchar da ta fayyace irin abin Ashshan da mata masu aikin kwana keyi wasu ma matan aure ne. inda lakchar tayi yawo sosai a shafukan sada zumunta.

Awannan karon ma’aikatan lafiyan reshen jihar kano karkashin jagorancin shugaban kungiyar Comrade Ibrahim mai karfi sunyi kira ga malamin da ya gaggauta janye Kalaman sa ya kuma basu hakuri ko kuma su dauki mataki a wata hira da yayi da Jaridar radio.

Advertising
Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button