Advertising
Advertising
Labarai

Ministan sadarwa Sheikh Isah Ali Pantami ya karbi wasika ta musamman daga wata yarinya

Ministan sadarwa Sheikh Isah Ali Pantami ya karbi wasika ta musamman daga wata yarinya

Kamar yadda shahararran marubuci Datti Assalafiy ya wallafa wani rubutu a shafin sa na sada zumunta Facebook, kan wata yarinya da ta aika wasika ga Ministan sadarwa Sheikh Isah Ali Pantani tana jinjina masa kan kokarin da yake.

Advertising

Datti Assalafiy ya wallafa rubutun kamar haka.

MINISTA PANTAMI YA KARBI WASIKA TA
MUSAM MAN DAGA WATA YARINYA.

Yarinyar me suna Laura Ogundele Wanda ta samu rakiyar Mahaifiyarta, sun gabatar da wasikar data rubuta wa mai Girma Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani Professor Isa Ali Pantami.

Advertising

Laura Wanda ta rubuta a cikin wasikar, ta
bayyana Minista Pantami a matsayin Kyauta ta musamman da Allah yayiwa Nigeria, “Duk lokacin dana kalli Minista Pantami sai na Hango shi a matsayin Shugaban Kasa” injiLaura.

Ta Rubuta Yaa Mista Pantami Ina Mai Godiya.

Da kasancewar ka minista mai hazaka a kasata Nigeria kuma ka kasance Zakaran Ministoci kuma ka kasance Kyauta ta musamman ga Nigeria.

Daga: Laura (Kawarka).

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button