Advertising
Advertising
Labarai

Babu wanda zai yi magana akan abin da Dr Abdallah Gadon Kaya ya fada ga Likitoci sai munafuki makiyin gaskiya, daga Datti Assalafiy

Kamar yadda kuka sani a ‘yan kwanakina nan Sheikh Abdallah Gadon Kaya ya fadi wata magana akan Likitoti na cewa, bai dace mutum yana barin matar sa tana tafiya asibiti wajan aikia kwana ana hada su da bamiji a ofishi daya ba.

Advertising

Wanda hakan yasa Likitocin suka yiwa maganar tasa wata fashimta ta daban wanda har suka yi magana akan ya janye wannan kalami nasa.

Daga baya Sheikh Abdallah Gadon Kaya ya fito ya yi cikekken bayani tare da wayarwa mutane kai akan maganar da ya fada kan Likitoci, domin da yawan mutane basu fashimci mai yake nufi ba a maganar da ya fada kan Likitocin.

To a yau kuma shahararran marubucin nan Datti Assalafiy ya wallafa wani rubutu a shafin sa na sada zumunta instagram, inda yake yabon Sheikh Abdallah Gadon Kaya kan fitowar da yake yana fadan gaskiya akan abunuwan da basu bace ba ba tate da jin tsoron kowa ba.

Advertising

Mai magana Datti Assalafiy ya wallafa rubutun a shafin nasa kamar haka.

Marigayi Sheikh Albaniy Zaria ya taba fadin wasu kalmomi na yabo da jinjina wa Sheikh Dr Abdallah Usman Gadon kaya tun yana raye, Malami ne da baya jin tsoron bayyana gaskiya akan abinda ya fahimta tun tashinsa.

Kafln fitinar ‘yan bindiga a jihohin Zamfara, Sokoto da Katsina tayi tsamari Sheikh Dr Abdallah sai da ya fito ya shaidawa duniya cewa, akwai sa hannun manyan mutane a cikin ta’addancin, a lokacin da yayi maganar sai da na ga wani bunsuru zindiki yana cewa wai ya kamata DSS su kama Dr Abdallah, yau yana raye
kuma maganar ta bayyana gaskiya.

Wannan Malamin ba dan duniya bane, Allah Ya sa a gaba kuma Allah ya sanya wa harcensa albarka sakonsa yana isa inda ya dace, marassa gaskiya da sauran munafukai hankalinsu na tashi, babu mai yiwa maganar Malam Abdallah akan mata Likitoci tawili sai makiyin gaskiya ko munafuki ko wanda halinsa ne hakan aka tona asiri.

A kaf maganganun da Malam yayi ba inda ya kama suna bai kama sunan garin su kowa ba, kuma ko da suka nemi su kalubanceshi ba wai ya janye maganarsa bane cewa, yayi bai fahimci tsarin aikin Asibiti a Kano ba kamar yadda suma basu fahimci maganganunsa ba.

Malam yayi abinda ya dace, kuma sako ya isa ko’ina duk wani mabarnaci da yake barna da matan mutane a Asibiti zai shiga taitayinsa, don ya san yanzu za’a sa ido ko ba don Allah ba.

Daga karshe Datti Assalafiy ya kara da cewa, Malam Abdallah Allah ya saka maka da gidan Aljannah.

Advertising

One Comment

  1. The very next time I read a blog, I hope that it does not fail me just as much as this one. I mean, I know it was my choice to read through, however I really thought you would probably have something interesting to talk about. All I hear is a bunch of moaning about something you could fix if you were not too busy searching for attention.} {visit site|visit my web site|visit the following page|visit site|visit the following webpage|visit|visit link|visit my home page|Visit Home Page|visit the following site

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button