Advertising
Advertising
Labarai

Wata budurwa mai suna Sumayya ta rubuce Al-Qur’ani mai girma da hannun ta cikin wata 3

Wata budurwa mai suna Sumayya ta rubuce Al-Qur'ani mai girma da hannun ta cikin wata 3

Wata matashiyar budurwa mai suna Sumayya Shu’aibu Salisu mai shekaru goma sha tawai 18, ta mokarin rubuce Alkur’ani mai girma da hannun ta a cikin wata uku 3 ba tare da da hannun kowa ba.

Advertising

Sumayya daliba ce wacce take aji uku 3 a babbar Sakandire wanda a yanzu haka ta sake aniyar rubuta Alkur’ani mai girma a karo na biyu.

Sumayya wacce ‘yar asalin garin Zaria ce an haife ta a garin Jega dake jihaf Kebbi, inda ta fara karatu a birnin Madina da ke Saudiyya a saa’ilin da mahaifinta Sheikh Shu’aibu Salisu yake zaman koyon karatu a Jami’atul Madina.

A lokacin da Sumayya take zantawa da Aminiya a Zaria ta bayyana cewa, bayan da na haddace Al-Qur’ani na kasance mai cike da burin ganin na kuma rubuta shi da hannu na, don haka na sa lokaci kuma na fara.

Advertising

Sannan ta kara da cewa, Na kwashe tsawon watanni uku ina rubutawa kuma hakan na da nasaba ne da karancin lokaci da nake da shi, kasancewar har yanzu ni daliba ce yar aji biyu a Babbar Sakandire ga kuma koyarwa ina yi a Al-Mu’assasa Al-Islah Foundation, makarantar da mahaifina ya assasa a Unguwar Dan Dutse da ke yankin Sabon Layi a Tudun Wadar Zaria.

Sumayyah ta kasance Alarammiya ga Mahaifinta a lokacin gabatar da tafsir na watan Ramadan musamman a lokaci da aka sa dokar hana fita sakamakon bular annobar cutar Coronavirus a shekarar 2020, inda take ja masa baki yana fassarawa, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

Sumayyah tace tana da sauran buri a rayuwarta inda take bayyana cewa, ina so in zama kwararriya a kan ilmin Komfuta, sannan in kasance shahararriyar malamar addinin musulunci mai sanar da mutane kalmar Allah.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button