Wani magidanci ya fashe da kuka tare da rungumar Matar sa bayan ta biya bashin da ake bin sa naira N1.3M
Kamar yadda matar mutumin take bayyana cewa, mijin nata ya dau tsawon shekaru yana biyan bashin da ake binsa duk wata, amma duk da haka bai gama biya ba.
Yayin da matar ta kira mijin nata cikin dakin su don ta shaida masa cewa ta biya sauran bashin da ake bin shi da kudin da take tara wa, nan take ya fashe da kuka don tsananin farin ciki.
Wanda matar ta sake bayyana cewa, mijin tana ya aro kudade daga banki na tsawon shekaru uku domin ya dauki nauyin su.
Sannan ta kara bayyana cewa, mijin nata ya dauki tsaron lokaci yana biyan kudaden da ake bin sa a duk karahen wata, inda ta kara da cewa ta dade tana rokon ubangiji ya hore mata kudin da zata biyawa mijin nata bashin da ake bin sa.
Kamar yadda matar ta fada da bakin ta cewa, Na dade ina taru sabida inaso inga mijina a farinciki, Inaso inga hankalin shi ya kwanta daga fadi tashin da yake, bayan ta samu cikkaken bayani game da yawan kudin da ake bin mijinta, ta gane cewa akwai sauran N1,372,624.69 da ya kamata ta biya. Sai kawai matar ta biya duka.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuga irin murna da farin cikin da mutumin yake bayan matar tasa ta biya masa bashin da ake bin sa.
Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.