Labarai

Hukumar NDLEA ta gano Naira biliyan 4.200 a bankin Abba Kyari

Hukumar NDLEA ta rubutawa Minstan Shari’a na Najeriya Abubakar Malami takarda a makon jiya inda take neman a bata umarnin kotu domin ta kwace kadarorin fitaccen mukadashin kwamishinan ‘yan sanda DCP Abba Kyari wanda a yanzu yake hannun hukumar bisa zargin sa da ake da hannu a badakalar miyagun kwayoyi.

Hukumar sha da fataucin miyagun kwayoyi ta gano wasu kudade naira biliyan 4.200 da take zargi na miyagun kwayoyi be a asusun ajiyar banki na DCO Abba kyaryda da mataimakinsa ACP Sunday Ubua, inda nair biliyan 1 da miliyan 400 suka shiga asusun ajiyar Abba Kyari a lokacin da yake jagorancin rundunar ‘yan sanda IRT, ragowar naira biliyan biyu da miliyan dari takwas kuma suka shiga asusun mataimakinsa ACP Sunday Ubua.

Hukumar tace rundunar ‘yan sandan ta IRT a lokacin da Abba Kyari ne shugabanta ta kwace miyagun kwayoyin tramadol da kudinsu ya kai Naira biliyan uku, kuma a daidai lokacin be kudi naira miliyan 2 da dubu 600 da dubu 4 ya shiga asusun mataimakin Abba Kyari na rundunar ACP Sunday Ubua wanda a lokacin ya sayi hannun jarin naira miliyan 100 na wani banki, lamarin da yasa hukumar je zargin an yi watandar kwayar taramadol tramadol din ga dilallan miyagun kwayoyi.

A halin yanzu a zaman kotun da aka gudanar matar abba kyari ta yanke jiki ta wadi inda aka dakkota aka fita da ita zuwa asibiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button