Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya kafa sabuwar dokar hana dabancin siyasa da manna fastoci a jihar
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya kafa sabuwar dokar hana dabancin siyasa da manna fastoci a jihar
Gwannan jihar Katsina Aminu Bello Masarai ya sanya hannu a wata sabuwar doka da ya fitar na yunkurin magance matsalar tsaro a jihar ta sa.
Yahaya Sirika wanda Kwamishinan yada labarai ne da Al’adu na jihar jihar Katsina, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a a Katsina.
Yahaya Sirika ya bayyana cewa, gwamnan Masari ya yi amfani ne da sashi na 176(2) na kundin tsarin mulkin kasa na 1999 da ya baiwa gwamnan jiha ikon yin doka a kan kansa, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
A cewar sa, dokar wacce ta fara aiki tun 1 ga watan Janairu, ta yamma dukkanin wani nau’i na dabancin siyasa da aikata wasu laifuka makamantan hakan.
Sannan Kwamishinan ya kara da cewa, dokar ta kuma hana manna fastocin siyasa a gine-ginen gwamnati ofisoshi da sauran guraren jama’a a jihar.
Kuma yace, dokar ta hana duk wani taro na ‘yan baranda siyasa da suka hada da Bacha, Ƙauraye, koma wanne irin suna a ke kiransu da zai razana al’umma a jihar.
Sannan kuma Sirika ya yi gargadin cewa, duk wanda ya saba dokar za’a kama da kaifin karya sashe na 114 na dokar ‘penal code’ ta jihar.