Labarai

Kotu ta dage shari’ar Abduljabbar zuwa 3 ga watan Maris domin ya bada bayanan kariya

Kotu ta dage shari'ar Abduljabbar zuwa 3 ga watan Maris domin ya bada bayanan kariya

A ranar Alhamis ne Babbar Kotun Shari’a dake birnin jihar Kano ta sanya ranar 3 ga watan Maris a matsayin ranar da Malamin Addinin nan, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara zai bada bayanan kariya.

Kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, ana cigaba da Shari’ar Abduljabbar ne bayan da ake zargin sa da yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad S.A.W.

A’a na zargin Abduljabbar ne dai da Laifuka 4 da suka shafi yin kalaman batanci ga Ma’aiki.

Alkalin kotun Mai Shari’a Sarki Ibrahim Yola ne ya sanya ranar bayan da lauyan Abduljabbar Ambali Obomeileh Muhammad SAN, ya roki kotun da ta dage zaman domin a baiwa wanda yake karewa damar yin bayanan kariya.

Shi ne sai mai shari’a Sarki Yola ya dage zaman sai ranar 3 ga Maris domin cigaba da sauraron karar, a ranar 3 ga Fabrairu ne dai kotun ta baiwa Gwamnatin Kano da ta kira shaida na daya domin tuhuma.

A cigaba da shari’ar a ranar alhamis, lauyan gwamnati Suraj Sa’eda yazo da shaida na daya, PW1, Adamu Adamu, inda bayan ya gama yi wa Abduljabbar tambayoyi ne, shi ne kotu ta sallame shi ta kuma sanya 3 ga watan Maris domin wanda ake karar ya kare kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button