Advertising
Advertising
Labarai

Majalistar jihar Zamfara ta tabbatar da Hassan Nasiha a matsayin mataimakin Gwamna bayan tsige Mahdi Aliyu Gusau

Majalistar jihar Zamfara ta tabbatar da Hassan Nasiha a matsayin mataimakin Gwamna bayan tsige Mahdi Aliyu Gusau

A ranar Laraba ne aka gudanar da zaman Majilistar Dokoku ta jihar Zamfara inda har aka tsige mataimakin gwamnan jihar “Mahdi Aliyu Gusau.

Advertising

Sai kuma jim kadan bayan bayan tsige mataimakin gwamman “Mahdi Aliyu Gusau”, sai Majalisar Dokokin ta jihar Zamfara ta tantance “Sanata Hassan Nasiha” a matsayin sabon Mataimakin Gwamna jihar.

Kamar yadda a yanzu aka tabbatar da cewa, Hassan Nasiha shine Sanata mai wakailtar Zamfara ta tsakiya a Majalistar Dattijai.

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito cewa, ‘yan majalisar sun tabbatar da Hassan Nasiha a matsayin sabon Mataimakin Gwamna a wata kuri’a ta bai daya.

Advertising

Gwamnan Jihar “Bello Matawalle” a cikin wata wasika daya rubutawa Sakataren Gwamnati “Kabiru Balarabe” wanda shine Kakakin Majalisar, inda Nasiru Magarya ya karanta a zaman majalistar a ranar Laraba, ya mika sunan Hassan Nasiha a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar bayan cire Mahdi Aliyu Gusau da aka yi.

Sai kuma Shugaban Masu Rinjaye wato “Faruku Dosara” shima ya mika kudurin tabbatar da Hassan Nasiha a matsayin mataimakin gwamnan wanda dukka mambobin suka amince.

Sannan kuma Kakakin Majalisar ya bayyana cewa, nadin sabon Mataimakin Gwamnan ya yi daidai da tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin kasa na shekarar 1999.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button