Rahama Sadau ta sadaukar da kudaden da take samu a shirin ta mai suna “Nadeeya” ga marasa karfi
Rahama Sadau ta sadaukar da kudaden da take samu a shirin ta mai suna "Nadeeya" ga marasa karfi
Kamar yadda kuka sani ficacciyar jarumar masana’anyar kannywood da Nollywood Rahama Sadau tana haska wani fim din ta mai suna “Nadeeya”, wanda ya sami karbuwa a wajan al’umma duba da yadda ta tsara shirin.
To a yau kuma mun sami wani labari kan abin alkairin da jaruma Rahama Sadau ta yi ga marasa karfi da , inda ta sadaukar da kudaden da take samu na shirin nata mai suna “Nadeeya” ga marasa karfi.
A shirin da Jaruma Rahama Sadau tayi da Main Hun Khan cikin shirin LARKI LARKA a tashar Liberty Radio 103.3 FM Kano jarumar ta sadaukar da dukkannin kudin da sabon film dinta NADEEYA ya kawo a Cinema cikin gidauniyar tallafawa marasa karfi ta RAY OF HOPE. Allah ya saka mata da alheri.
Main Hun Khan wanda ya gabatar da shirin yayi rubutu inda ya tabbatar da cewa rahama sadau tayi wannan alkawali na taimawaka marasa karfi da duk kudin da shirina nadeeya ya kawo a cinema wanda haryanzu ana kallonsa a cinema.
Masha Allahu a hirar da nayi da rahama sadau yau wanda ta sadaukar da abinda ta samu na film dinta da ake haskawa acikin kwana kenan ga marayu da gajiyayyu.