Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un: Allah ya yiwa ‘yayan jarumi Alhaji Balarabe Jaji rasuwa sanadiyyar hatsarin mota
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un: Allah ya yiwa 'yayan jarumi Alhaji Balarabe Jaji rasuwa sanadiyyar hatsarin mota
Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, yanzu-yanzu muka sami labarin rasuwar ‘yayan tsohon jarumin masana’antar kamnywood Alhaji Balarabe Jaji, a hatsarin mota daga Kaduna zuwa Jaji.
Kamar yadda shafin kannywoodcelebrieties dake kan dandanlin sada zumunta na instagram suka wallafa labarin, suna mai cewa.
lnnalillahi wa inna ilaihiraji’un: ALLAH YA JARRABI ALH. BALARABE JAJI da mutuwar ‘ya ‘yan sa guda hudu 4 sanadiyyar hadarin mota daga Kaduna zuwa Jaji, Muna musu addu’a Allah yajikansu da rahama ya kyauta makwanci Amin.
Mahaifin su, kuma Alh. Balarabe Jaji, mahaiflyar su da yan uwansu Allah ya basu hakuri da juriya na rashin wadan nan ‘ya’ya nasu , Allah ya san zaka iya daukar jarrabawan da ya maka dan haka kayi hakuri, idan kayi Kanada riba mai girma a ranar gobe kiyama, Allah yasa muyi kyakkyawan karshe Amin.
Muna a matsayin mu na masu wannan shafin “Hausadailynews” muna rokon Allah ya gafar ta musu Allah ya sa bakin wahalar su kenan, idan tamu tazo Allah ya sa mucika da imani. Ameen