Wasu matasan ‘yam Mata 2 a jihar Sokoto sun fito takara a matsayin Gwamnan jihar a zaben da za’a yi 2023
Wasu matasan 'yam Mata 2 a jihar Sokoto sun fito takara a matsayin Gwamnan jihar a zaben da za'a yi 2023
Har yanzu dai ana samin matan da suke da ra’a yin shiga harkar siyasa domin ganin sun mallaki wani mukamin, inda wasu ma suke harin kujerar gwamnati.
To a yau ma dai mun sami wani labarin matadan ‘yam mata guda biyu 2 wanda suka bayyana ra’a yin su na tsayawa takarar neman kujerar gwamnati a jihar Sokoto.
Wata matashiya mai suna Farida Labaran Yusuf ta bayyana ra’ayin ta na tsayawa takarar Gwamnan jihar Sokoto a zaben da za’a gudanar na shekarar 2023, dake tafe a karkashin jam’iyar PDP mai ci a jahar Sokoto.
A yanzu haka shafin sada zumunra na Facebook na Farida labaran Yusuf har ma ta mayar da shi excellency Farida labaran yusuf, domin al’umma su yarda abin bada wasa take ba.
Bayan haka a bangare guda Farida Labaran ta zabi yar uwar matashiya Hajaru Muhammad mai dambun kaza a matsayin mataimakiyar ta.
Wadannan matasan ‘yam matan guda biyu 2 Farida Labaran Yusuf da kuma mataimakiyar ta Hajaru Muhammad, sun fito takarar ne a Jam’iyyar PDP mai alamar Lema a jihar Sokoto.