Advertising
Advertising
Labarai

Zan fice daga jam’iyyar PDP kafin karshen wannan watan na Maris ya kare, cewar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

Zan fice daga jam'iyyar PDP kafin karshen wannan watan na Maris ya kare, cewar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Kamar yadda kuka sani a kwanakin baya labari ya yu ta yawo kan cewa, tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso sun kafa wata kungiya mai suna “TNM”, domin dora al’umma kan shugabanci na gari.

Advertising

Wanda har gidan jaridar BBC Hausa suka wallafa bidiyon yadda Kwankwaso yake bayani kan wannan kungiya tasu da suka kafa ta “TNM”.

To a yanzu ma dai mun sake cin karo da wani labarin kan cewa, Rabi’u Musa Kwankwaso zai koma jam’iyyar “NNPP”, wanda a yanzu ya yanke shawarar barin tsohuwar jam’iyyar sa ta “PDP” kamar yadda BBC Hausa suka wallafa cikekken labarin kamar haka.

Tsohon gwamnan jihar Kano dake Arewacin Najeriya kuma jigo a jam’iyyar PDP mai hamayya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce zai fice daga jam’iyyar kafin karshen wannan watan na Maris.

Advertising

Tsohon gwamnan ne ya tabbatar wa da BBC Hausa wannan Iabari inda yame cewa, ya yi nisa a shirinsa na komawa jam’iyyar NNPP watau New Nigeria Peoples Party.

Wani makusancin tsohon gwamnan yace, babu tsari a game da yadda ake tafiyar da sha’anin jam’iyyar ta PDP, Iamarin da ya tilasta wa Sanata Kwankwaso tattara kayansa domin ya fice daga cikinta.

A watan jiya ne Kwankwaso ya jagoranci wani gagarumin taro na wasu manyan siyasar kasar karkashin wata kungiya mai suna The National Movement “TNM”.

Fitattun mutane da yan siyasa da suka halarci taron sun hada da Alhaji Tanko Yakasai da Capt Idris Wada, tsohon gwamnan Kogi da Rufai Alkali da Aminu Ibrahim Ringim, tsohon dan takarar gwamna a jihar Jigawa da kuma Inijiniya Buba Galadima.

A baya dai, Sanata Kwankwaso ya nuna rashin jin dadinsa game da yadda jam’iyyar PDP take kokarin mayar da shi dan bora duk da gudunmawar da yake bayarwa a cikin jam’iyyar.

An dade ana kai ruwa rana tsakani tsohon
gwamnan na Kano da bangaren tsohon ministan harkokin waje, Aminu Wali.

Kwankwaso ya koma jam’iyyar PDP ne daga
jam’iyyarAPC bayan zaben shekara 2015, sakamakon takun-sakar da aka rika yi tsakaninsa da wanda ya gaje shi, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

A shekarar 2019, ya tsayar da tsohon Kwamishina a gwamnatinsa, Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP na gwamnan jihar ta Kano, k0 da yake ya sha kaye a hannun Gwamna Ganduje.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button