Wani yaro ya shiga matsanancin hali bayan da wani marar imani ya yanka masa wuya a makaranta
Kamarin yaron da aka yanka wuyansa a cikin makaranta a ranar 15 ga watan janairun 2022 mai suna Jibrin Sadi Mato wanda ake masa lakabi da Ramadan, ya shiga mawuyacin hali wanda a yanzu yana asibitin Nizamiye dake Abuja.
Ramadan wanda yake da shekara sha 11 mai suna an yanka wuyan sa ne a ranar sha biyar 15 ga watan da ya gabata na janairu, a makarantar Elkanami dake maiduguri a jihar Borno kuma ana zargin siniyan sa ne da yunkurin kisan kan.
Biyo bayan zargin da ake na siniyan sa ne ya aikata masa danyan aikin ya nemi hallaka shi gwamnatin jihar ta kafa kwamitin bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru, sai dai har yanzu ba’a sami cikakken sakamako ba daga kwamitin binciken.
cewar ‘yan uwan Ramadan sun gaji da jiran gawan shanu a halin yanzu yan uwan nasa suna cigaba da fadada zargin su, inda zargin ya biyo ta kan asibitin da suka yiwa Ramadan aikin wuyan sa wato asibitin koyarwa ta maiduguri inda suka gano cewar.
kamar akwai kulla-kulla cikin aikin da aka yiwa Ramadan sabida a halin yanzu yana wani babban asibiti a birnin tarayyar abuja, inda likitocin suka alakanta aikin wuyan nasa da babban al’amari kamar yadda hukumar asibitin tace basu taba karo da case irin na Ramadan ba.
Sai dai a lokacin da asibitin sukayi yunkurin sake wa Ramadan sabon aiki a wuyan sa sun tabbatar da cewar, ya rasa wani sashe wanda ba lallai wannan bangaren ya kara samun waraka ba.