Labarai

Sheikh Aminu Daurawa ya fadi irin hukuncin daya kamata ayiwa mutumin daya kashe Hanifa ta hanyar bata guba

Sheikh Aminu Daurawa ya fadi irin hukuncin daya kamata ayiwa mutumin daya kashe Hanifa ta hanyar bata guba

Sheikh Aminu Daurawa ya yi magana akan kisan gillar da Abdulmalik ya yiwa Hanifa inda yake cewa.

Abin daya faru a jihar kano an wannan mutumin daya kashe yarinya ‘yar shekara biyar 5 wannan abin da tada hankalin kowa har shugaban kasa ma sai da yayi ta’aziyya akan wannan.

Malamin ya kara da cewa, tun da yake ko a tarihi bai taba ganin abin tausayi ba wanda aka yi a zamanin sa wanda ya kai wannan ta’addanci ba, wato kisan Hanifa da aka yi kenan.

Ya kara da cewa, ace malamin makaranta ya dauki dalibar sa wanda har wasu ma suna cewa shine shugaban makarantar, wanda yake koyar da su boko amma har ya nemi kudi a wajan iyayan ta aka bashi Miliyan uku 3 a cikin kudin amma yaje ya kashe yarinyar kuma ya daddatsata ya zuba ta a buhu.

Malamin yace bai taba ganin ta’addanci irin wannan ba sannan yace amma wannan sako ne a gare dukkan mu.

Sako na farko shine zuwa ga gwamnati: Lallai idan irin wannan ta haru ayi gaggawar kashe wanda ya aikata laifin, tayi masa hukunci sabida baza’a sha wahala ba wajan kyas din tun da ya fada da bakin shi ya aikata laifin kuma duniya taji.

Kuma irin wannan kamata ya yi a kai su wajan alkali tun da wuri a yanke musu hukunci sannan kuma hukuncin da aka yanke musu kowa yasan anyi.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji sauran bayani daga bakin Sheikh Aminu Daurawa.

https://youtu.be/u-iCOIYP_I4

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button