Advertising
Advertising
Labarai

Wata Budurwa ta sha guba ta mutu a ranar auren ta bayan sabida iyayan ta sun aura mata saurayin da bata so

Har yanzu dai ana samin ‘yam matan da suke hallaka kan su sabida da soyayya, inda yake yanke wa kan su hukunci ba kai tsaye ba tare da neman shawara ba.

Advertising

A wani labari da muka samu a yau din nan kan cewa, wata Budurwa ta Kashe kanta Sanadiyyar shan guba a cikin Abinci a Ranar Alhamis a garin Agalawar Balan da ke Karamar Hukumar kabo A jihar Kano.

Budurwar mai suna Zainab ta dauki mummunan matakin ne na kashe kan ta sabida an ki bata saurayin da take kauna a matsayin mijin ta, inda aka daura mata aure da wanda bata san shi.

A Tattaunawar da aka yi da Ado mai Nika makwabcin garin ya shaida cewa, Budurwar Zainab ta sha gubar ne sabida ba ta son saurayin da Iyayen ta suka daura mata aure da Shi.

Advertising

A wani bangare kuma an bayyana cewa, kawar amaryar ita ce ta sakawa amaryar guba a cikin abinci sabida bakin cikin kawarta Zainab ta sami miji ita bata samu ba, tuni dai aka nemi kawar amaryar aka rasa ta gudu daga garin zuwa wani wuri wanda ba’a sani ba.

Duk da dai dagacin garin ya dauki matakin kashe maganar a cikin gida hakan ya sa suka ki sanar da Jamiā€™an tsaro, amma yanzu dai maganar ta kai ga kungiyar rigar yanci International ta tsoma baki.

Yanzu haka dai kungiyar mai rajin kare hakkin dan adam ta kasa karkashin jagorancin shugabanta na jihar Kano Kwamared Usman A Usman tace, ta dukufa dan gano sahihin abin da ya faru tare da mika batun zuwa ga manta sabo.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button