Advertising
Advertising
Labarai

‘Yan Boko Haram sun kai hari sassanin Sojoji a jihar Kaduna inda suka kashe Sojoji 11 da raunata 19

'Yan Boko Haram sun kai hari sassanin Sojoji a jihar Kaduna inda suka kashe Sojoji 11 da raunata 19

A wani labari da muka samu daga shafin Daily Nigerian Hausa sunji cewa, Yan ta’addan Boko Haram sun kai hari a wani sansanin soji da ke unguwar Polewire a Birnin Gwari, Jihar Kaduna, inda su ka kashe sojoji 11 tare da jikkata wasu 19.

Advertising

Hakazalika wasu ‘yan kungiyar ‘yan banga uku ma sun rasa rayukansu, yayin da wasu biyu suka samu raunuka yayin harin.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa, a yakin da aka kwashi tsawon sa’o’i 3 da rabi wanda aka fara da karfe 4:30 na yamma kuma aka kare da karfe 8 na dare, an kona wasu manyan tankokin yaki guda uku bayan sun kori sojoji daga wajen.

Majiyoyin tsaro sun ce, wurin shi ne babbar hanyar zirga-zirgar ‘yan ta’addan dake tsallakawa daga Naija zuwa Zamfara.

Advertising

A cikin rahoton lamarin, wanda wakilinmu ya gani kayan aikin sojan da aka rasa ko aka lalata sun hada da 1 Legion MRAP;1 Cobra APC; 1 Styer APC; bindigar injin DSHK; 2 HK 21 bindigogi;1 GPMG; da bindigogi 14 kirar AK47, bindigogi masu sarrafa kansu 3; Babura 10, da sauransu.

Ko da yake daga baya an karo sojoji daga
sansanin ‘yan gudun hijira dake Gwaska da karfe 9:15 na dare, amma babu tabbacin adadin wadanda suka mutu daga bangaren

K0 da yake daga baya an karo sojoji daga
sansanin ‘yan gudun hijira da ke Gwaska da
karfe 9:15 na dare, amma babu tabbacin
adadin wadanda suka mutu daga bangaren ‘yan ta’addan.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button