kalli wani Bidiyon dake nuna cewar ga wadda ta chanji Nafisat Abdullahi a fim din LABARINA.
Jarumar data taka rawa acikin shirin film din Alaqa zango na farko, wato Ummi Alaqa ka iya maye gurbin Nafisat Abdullahi acikin shirin labarina.
Wannan na zuwane bayan jaruma Ummi Alaqa ta hada hotonta dana Nafisat Abdullahi inda ta wallafashi a shafinta na sada zumunta a Instagram, wanda hakan yasa mutane sunyi tsokaci matuka.
Nafisat Abdullahi dai bazata cigaba da fitowa acikin shirin Labarina ba, sakamakon matsala dasuka samu da kamfanin Saira Movies wanda hakan ya tilastawa kamfanin canja jarumar da wata.
Saidai tun bayan da Ummi Alaqa ta wallafa hotonta dana Nafisat Abdullahi inda ta rubuta (wace irin rawa kuke ganin zan taka a gurbin Sumayya acikin shirin labarina).
Mutane sun bayyana ra’ayinsu inda mafi rinjaye sun nuna goyon bayansu inda suke fadin akwai yanayi na kamanni tsakanin Nafisat Abdullahi dakuma Ummi Alaqa sannan zata iyayin “acting” da jaruma Nafisat Abdullahi takeyi.