Advertising
Advertising
Labarai

Turkashi: Ya Allah duk inda kasa Buhari ranar lahira kasaka ni Cewar Dan Bilki Kwamandan

Ya Allah Duk Inda Ka Sa Buhari A Lahira Nima Ka Sa Ni Dan Bilki Kwamanda

Advertising

Shahararren Sojan Bakan Siyasa a jihar Kano, Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda, wanda ya shahara wajen kare manufofin Gwamnatin Muhammadu Buhari. Ya yi addu’a wadda da yawan mutane suke kallon abu Bai kamata ba, Dan siyasar yace duk inda Allah zai sa Buhari ranar lahira shima a sa shi.

Kwamanda ya furta wannan furuci ne a wani gidan Radiyo mai zaman kansa jiya a jihar Kano. ‘Yar jaridar ta ja hankalinsa da cewa,

“Duk fa inda Allah Ya sa Buhari ka ce?” sai ya amsa da cewa, “Duk inda Ya sa shi nima ya sa ni, a garin nan akwai wanda ba mutumin kirki ba ne amma an fadi abinda ya fi haka a kansa”.

Advertising

Tuni mutane suka ringa fadan ra’ayoyin su a game da wannan magana da sojan baka a siyaysa ya fada, Wasu suna cewa abin da ya fada ba komai bane soyayya ce, inda wasu kuwa cewa suke babu wata soyayya da zata sa kai irin wannan.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button