Labarai

Baza mu yarda da rashin adalci ba kan rabon mukaman da uwar jam’iyya zata yi, cewar Ibrashim Shekarau

Baza mu yarda da rashin adalci ba kan rabon mukaman da uwar jam'iyya zata yi, cewar Ibrashim Shekarau

A bangaren jam’iyyar APC mai mulki a yanzu a jihar Kano wanda Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranta ya bayyana cewa, ba zai yarda da rabon mukaman da uwar jam’iyya ta kasa zata yi tsakanin su da tsagin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba sai dai idan za’a yi gaskiya da adalci.

Kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, a cigaba da zaman sulhu tsakanin bangarorin guda biyu da suke ta gabza rikicin mallakar jam’iyyar tun bayan kammala zaben shugabannin jam’iyya.

A ranar Asabar ne Kwamitin riko na jam’iyyar APC ya kira jagororin guda biyu da suje babban birnin tarayya Abuja domin wata ganawa da za’a yi ta gaggawa.

Sannan bayan tashi da ga taron gaggawar da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin Mai Mala Buni Gwamnan jihar Yobe, jam’iyyar ta yanke shawarar tura wani kwamiti mai karfi zuwa jihar Kano domin tabbatar da anbi sabon tsarin rabon mukaman jam’iyyar daidai.

Bayan haka a wata takaitacciyar sanarwa bayan taron na jiya Asabar da aka gudanar da daddare, mai magana da yawun Shekarau Sule Ya’u Sule ya tabbatar da cewa, jam’iyyar ta samar da tsarin sanya kowa cikin harkokin jam’iyyar ta APC a jihar Kano.

Kamar yadda Suke Ya’u Sule ya fadi cewa,  a yau Litinin za, a sanar da duk bangarori biyun halin da ake ciki.

Wanda a jiya Lahadi ne Sahekarau ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankalin su sannan kuma su baiwa uwar jam’iyyar goyon baya, sannan ya kara da cewa zasu bi umarnin Ubangiji da kuma na jam’iyyar su yarda a yi sulhu da tsagin Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button