Advertising
Advertising
Labarai

Ko baka da gemu Allah zai baka lada idan niyyarka mai kyauce akan sa ba sai ka shafa magani ya fito ba

Kamar yadda kuka sani akwai mutane da Allah yake jarrabar su da son gemu ya fito musu amma sai kaga burin su bai cika ba, wato sun nemi gemun ya fito amma bai samu ba.

Advertising

Wasu ma ta dalilin kin fitowar tasa sukan sayi abin da zasu shafa a habar tasu domin gemun ya fito.

To a yau kuma mun sami wata tambaya da wani bawan Allah ya yiwa “Dr Jamilu Yusuf Zarewa” akan ya halatta mutum ya shafa cream domin gemun sa ya fito ya tsaida sunnah.

Ga dai tambayar da mutumin ya yiwa Dr Jamilu Yusuf Zarewa da kuma amsar da aka bashi.

Advertising

Assalamu Alaikum Allah ya qarawa Dr lapia ina da tambaya : Shin ya halatta mutum ya shafa cream, domin gemunsa ya fita Ya tsayar da SUNNAH ?.

Ga yadda aka bashi amsar tambayar sa.

Wa alaikum Assalam, zai fi kyau ya jira har Allah ya fito masa da shi, sabida amfani da magungunan da suke canza yanayin dan adam yana biyar da matsaloli a mafi yawan lokuta.

Allah yana iya baka ladan wanda ya tsayar da gemu ko da bai fito ba, mutukar niyyarka ingantacciyya ce.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button