Labarai

Tsohon Jarumin Nollywood Papa Ajasco Ya Rasu

Fitaccen kuma tsohon dan wasa Mista Ogunrombi ya shahara saboda rawar da ya taka a cikin fim din Papa Ajasco.

Jarumin a masana’antar shirya fina finai ta Nigeria Nollywood Papa Ajasco wanda ya juma yana bada gudun mawa a masana’antar, Ya rasu.

Wani mutun da ake kira da Hussaini Shehu shiya fitar da wani sako a shafin sa na Twitter eanda yake tabbatar da mutuwar dan wasan kwaikwayon.

Ya rubuta cewa, “A yanzu na samu labarin cewa masanin kida, tsohon mai koyar da waka  a NATIONALTROUPE kuma wanda ya fito a matsayin ‘Papa Ajasco’ a cikin shahararren shirin barkwanci na #waleadenugaprod ‘Papa Ajasco’, Mista Femi Ogunrombi ya rasu.

“An sanar da ni cewa dan wasan kwaikwayon, mawaki, babban jarumi kuma kwararren ma’aikacin jinya wanda muke kira ‘Uncle Ogurombo’ ya rasu a Yammacin yau (Asabar).”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button