Asiri ya tonu: Saurayi ya kwana da budurwar sa a kango daga zuwa zance.
Wani saurayi da yaje zance, ya tafi da budurwar wani kango sun kwana sabo da a cewarsa dare ya yi kuma yana tsoron kar taje garin shiga gida ta hadu da wani abun.
Kana iya bayyana ra;ayinka a kai, ka kuma tara a cikin shirin Baba Suda na yau domin jin cikkaken labarin.
Labarin wani Saurayi da budurwar sa.
Saurayinta ya zo gaishe da iyayenta, aka Kai shi wajen tarɓar baƙi. Sun fara hira ke nan, sai ƴar aikin gidan ta kawo musu Lemo da Pizza.
Ya sanya hannu ya ɓantari Pizza ya fara ci. Ta ce, Ka ji daɗinta kuwa? Ya ce, sosai ma kuwa.Ta ce, Ni nayita, na sha wahala sosai, duk don na burgeka.
Umma ce ta kai ni wajen wasu ƙwararru, ta kashe kuɗi masu yawa suka koya mini, kuma fa na koya ne saboda kai kaɗai..!!
Ya ce, wallahi ta yi daɗi sosai, nagode da wannan hidima d kika yi, lalle in na aureki bani da matsalar abinci, na yi murna sosai, tabbas kin ƙware wajen sarrafa abinci…!!!
Bayan ya tafi, ta je ta samu Babarta ta ce, a ina kuka samo Pizza mai daɗi haka? Babarta ta ce, ai saurayinki ne ya kawo ta, shi ne na gutsuro muku..!