Advertising
Advertising
Labarai

Duk Mace Mai Cikakkiyar Tarbiyya Ba Za Ta Taba Yin Ciko A Jikinta Don Ta Burge Saurayi Ba

Daga Comr Abba Sani Pantami

Advertising

Ya kamata mu sani duk wani mai hankali da yake son ya Auri mace mai tarbiya, wallahi bazai taba maida hankalinshi akan zallar siffofin budurwar ba, musamman ma budurwar tana da tarbiyar Addini, saboda shi zai Aure tane domin tarbiyar ta.

Yawanci idan kuka lura duk budurwar da take ciko don ta dinga bayyana surorin jikinta ga Maza galibinsu irinsu suke Aura (karya ta hadu da karya) bayan Aure da kwanaki kadan kaga anata rikici.

A shekarar da ta gabata irin wannan abun ya taba faruwa da wani abokina, nasan zaiga wannan rubutun nawa, yaje wani gari biki garin yana kusa damu ya hadu da wata budurwa itama duk tayi ciko tayi matukar burgeshi ya karbi lambarta suka fara soyayya har takai ga anyi Aure.

Advertising

Kwana guda da tarewarsu rikici ya barke a tsakanin su, iyaye sun shiga tsakani amma ya kasa yin hakuri karshe dole rabuwa suka yi, bayan lamarin ya faru da kusan wata biyu na hadu dashi yake bani labari na tambayeshi amma Don Allah me yasa duk da iyaye sun baka hakuri amma baka hakura ba, ya ce mun wallahi bazai iya zama da ita ba a matsayin Matarshi ba saboda ta cuceshi ta yaudare shi, duk yadda yayi zaton zai ganta ba haka ya ganta ba, a duk lokacin da ya kalleta tsananin bakin ciki ne yake ji a ranshi, ya yita kokarin ya hakuri amma ya gagara.

Irin wa ‘yan nan matsalolin musamman ma a wannan zamanin suna daga cikin abubuwan da suka fi komai kashe Aure, yawanci Maza sun ajiye batun tarbiya a gefe sun koma Auran sha’awa, matan suma sun daina tsoron Allah sun koma jan hankalin samari da surar jikin su. Kowane Namiji na tabbata yana da kalar macen da yake son ya Aura wata kila ma cikon da za kiyi wani baison yadda kika koma, wani a irin siffar da Ubangiji ya miki ba tare da kinyi ciko ba, shi irinki yake son ya Aura.

Na yi imani da Allah duk Namijin da ya Auri mace saboda surar jikinta, bayan Aure yagane abubuwan duk bogine wallahi ko bai rabu da ita ba, daga lokacin sai dai a fara zaman hakuri, kuma babbar matsalar cikon da matan suke yi yayi muni da yawa. Allah ka shiryar damu, ka cigaba da tsare mana imaninmu ka bamu Mata Nagari masu tarbiya.

Advertising
Back to top button