Labaran Kannywood
Sabon Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya nada Abba El-mustapha a matsayin Shugaban tace fina finai na kannywood
Sabon Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya nada Abba El-mustapha a matsayin Shugaban tace fina finai na kannywood
A kwanakin nan ne majiyarmu ta samu labarin daga Premier Radio kano labarin cewa Abba Elmustapha ne ya samu zama shugaban tace fina finai a jihar kano (chairman censorship board)
Advertising
Abba El-Mustapha1 dai guda ne daga cikin jaruman fina-finan Hausa na Kannywood wanda ya jima a tsarin siyasar Kwankwasiyya.
Daman dai tuni hankula suka karkata kan wanda za’a bawa hukumar, yayin da wasu ke tunanin za’a bawa Sunusi Oscar 442, kasancewar yana cikin na gaba-gaba a sha’anin siyasar ta Kwankwasiyya a Kannywood.
Wasu daga cikin jaruman Kannywood dai sun sha fuskantar dauri a gwamnatin baya, abinda aka alakanta da yadda ake zarginsu da nuna zazzafar adawar siyasa ga tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje na APC a wancan lokaci.
Advertising
Advertising