Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Mai neman suna idan ka isa ka bugi kirji ka kira suna, martanin Nafisa Abdullahi ga Sarkin Waka

Mai neman suna idan ka isa ka bugi kirji ka kira suna, martanin Nafisa Abdullahi ga Sarkin Waka

Kamar yadda kuka sani a jiya ne mawaki Nazir M Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin waka ya yi wata magana dangane da ‘yan masana’antar kannywood kan cewa.

Advertising

Idan ana neman ‘yayan sa aka haifa wanda ba’a kula da su to azo masana’antar kannywood, wanda maganar tasa ta biyo baya ne a lokacin da jaruma Nafisa Abdullahi tayi magana akan iyayan da suke haifa yara basa iya kulawa da su sai dai su tura su Almajiranta.

Bayan wannan magana da Naziru Sarkin Waka ya fada akan ‘yan masana’antar kannywood din sai ake gamin kamar ya maida martani ne ga Nafisa Andullahi kan abin data fada.

To a yanzu kuma jaruma Nafisa Abdullahi ta maida martani kan wannan magana da Naziru Sarkin waka ya fada ga su ‘yan kannywood din, wanda har take nuna cewa idan ya isa ya kama sunan da wanda yake.

Advertising

Jaruma Nafisa Abdullahi ta yi martani mai zafi ga Sarkin Waka kan wallafar da yayi na kare iyayen da ke haihuwar yara su barsu suna Almajiranci, inda jarumar ta kira Naziru Sarkin Waka da mai neman suna.

Ta kara da cewa, ta san matsalar sa kuma idan ya isa ya bugi kirji ya kira suna ne, kwatsam sai ga wallafar Sarkin Waka inda yake bayyana cewa,

Ba Almajirai bane yaran da iyayen su suka haifa suka kasa kula da su ba, idan kana son ganin ‘yayan da iyayen su suka haifa kuma suka kasa kula dasu to ka taho masana’antar fim.

Jaruma Nafisa Abdullahi bata yi kasa a guiwa ba taje shafinta na Twitter inda ta yi wa mawakin martani inda ta kira shi da mai neman suna, idan kuma ya isa ya bugi kirji ya kira suna.

Inda tayi wallafar kamar haka.

Mai neman suna!!! Ka bugi kirji ka kira suna mana. Duk da dai na san matsalarka. Ramadan Kareem.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button