Advertising
Advertising
Labarai

Fauziyya D sulaiman tayi cikekken bayani akan matan da suke bawa samari kansu da sunan soyayyar gaskiya

Maganin kar ayi kar a soma, babban kuskuren da mata suke yi akan aure daga Fauziyya D sulaiman.

Advertising

Fauziyya D sulaiman ta bayyana cewa ana yawan kai musu korafe-korafe wanda ba akan komai bane sai akan abin da yake faruwa a zamantakewar aure har ma abin yayi yawa.

Inda matan aure suke yawan kai musu koke-koke tun ma auren nasu bai je ko’ina ba, ma’ana shine matan da sukayi saban aure sune suke kaiwa wannan korafin, wanda aure masu bai wuce wata 2 wata 3 ba.

Da yawa daga cikin matan suna kaiwa karar mazajensu ne akan cewa suna takura musu basa barin su suna zuwa unguwa ko zuwa makaranta, inda wata ma take cewa mijin nata ya hanata chatting.

Advertising

Amma bayan wannan korafe-korafen da matan suke kaiwa akan musu tambayoyi wanda a tambayoyin da ake musu ana gane cewa, yawancin abin da yake kawo wannan matsalolin shine soyayyar shan minti.

Wannan soyayyar anayinta ne kafin aure wanda ‘yan matan yanzu suke daukan ta namiji ya kusance ki shine wayewa shine cigaba kuna hakan shine nuna soyayya.

Fauziyya D sulaiman tayi cikekken bayani a cikin wata bidiyo wanda muka samo ta daga tashar Youtube mai suna, Tsakar gida, wanda tashar ta shahara wajan wallafa bidiyoyi da kuma labarai.

Ku kalli bidiyon da muka ajiye a kasa domin kuji cikekken bayani daaga bakin Fauziyya D sulaiman, akan wannan korafe-korafen da mata suke yawan kai musu akan mazajensu suna hana su yin wasu abubuwan.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button