Advertising
Advertising
Labarai

An gano yaran da suka bata daga hannun iyayan su bayan fadada binciken Kwamitin Gwamnatin jihar Kano

An gano yara 4 da suka bata bayan fadada binciken Kwamitin Gwamnatin jihar Kano

Kwamitin da Gwamnatin jihar Kano ta kafa domin nemo wasu yaran da suka aka mena aka rasa, jihar Kano ya gano wasu yara hudu kuma tuni aka sada su da mahaifan su.

Advertising

Sakataren Gwamnatin jihar Kano Alhaji Usman
Alhaji shi ne ya karbi yaran a hukumance a
ofishinsa a jiya Juma’a.

Yaran da suka bayyana bayan rasa sun da aka yi sun hada da Abdullahi Yahaya mai
shekara 14, Umar Sani,12, Isma’ila Sabo 12,
da Isah Haruna mai shekara 13.

Shugaban kwamitin wada Umar Rano ne ya kai yaran inda yace, an gano su ne a jihar Legas da taimakon ‘yan sandan farin kaya wato DSS.

Advertising

Sannan yace, da aka gano yaran sai aka yi gwajin halittun su da na mutanen da suke rike dasu, sai kuwa sakamakon gwajin ya nuna ba
mahifansu ba ne.

Ya kara da cewa, tuni aka gano iyayen uku da ga ciki, dayan kuma ana nan a na neman mahifansa, inda yace tuni aka danka guda ukun a hannun mahaifan su inda ya yaba wa Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje bisa jajircewar sa wajen gano yaran.

Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa, a shekarar 2019 ne rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gano wasu yara 9 da aka sace aka kai su
garuruwan kudu, inda ta yi zargin an sayar da
su da canja musu addini lamarin da ya haifar
da cece-kuce a kasa baki daya.

Haka zalika iyayen yara suna fadin cewa, yanzu
haka a kwai yara sama da dari 100 da ba’a gan su ba.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button