Advertising
Advertising
Labarai

Yadda jami’a tsaro sukai Dabun gawar yan data karaya baya akalla 205.

Wani Rahoto ya bayyana cewa fiye da ‘yan ta’adda 200 sun rasa rayukansu a luguden wuta ta tsawon kwanaki hudu da jami’an tsaro suka yi musu a Jihar Neja dake Nigeria.

Advertising

Wakilinmu ya ruwaito cewa, jami’an tsaron da suka hada da sojoji, ‘yan sanda, Civil Defence da ‘yan sa-kai sun hallaka ‘yan ta’addan ne a Kananan Hukumomin Rafi, Mariga da Kontagora na jihar.

Kwamishinan Kanan Harkokin Masarautu da Tsaron Cikin gida Mai Suna Emmanuel Umar, ne ya tabbatar da hakan a wani taro kan lamarin tsaron jihar ta Niger, yana mai cewa kungiyoyin ‘yan bindiga hudu ne suke cin karensu babu babbaka a jihar ta Niger.

Kwamishinan yace ‘yan ta’adda da dama sun tsere da raunuka da harsashin bindiga a jikin su. Inda yayi kira ga al’umma da su ci gaba da taimaka wa jami’an tsaro da da yan sa kai wajen bayanan sirri wanda hakan zai taimaka wajen kawar da ‘yan Ta’addan da magance matsalar tsaro a Jihar.

Advertising

Kwamishinan ya fadi wasu manyan kungiyoyin ‘yan tada kayar baya hudu karkashin jagorancin Bello Turji, Yellow Janbros, Kachalla Halilu da Ali Kawaje.

Kwamishinan yace sun kwato babura da shanu da kuma awakai da dama, kari a kan bindigogi daga hannun yan ta’addan.

Yace Gwamnatin jihar ta dauki azamar sauya dabarun tunkarar ‘yan ta’adda kuma ta shirya kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi jihar cewar kwamishinan.

Source: Aminiya

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button