Ficaccan mawakin Kannywood Hamisu breaker ya shiga sahun gaba a samin maziyar ta na mawakan Nageriya 2021
Kamar yadda kuka sani ako wace an tantance mawakan da suka fi samin mabiya a sabbin wakokin su da suke rerawa, to a wannan shekarar ta 2021 Ficaccan mawaki Hamisu breaker yana sahun gaba wajan samin maziyarta a manhajar sa ta Youtube.
Dandalin Turntable Charts mai fitar da kididdigar wakokin da aka fi saurare da kallo a shafin na Youtube ne ya fitar da alkaluman.
Kamar yadda Voahausa ta ruwaito jerin mawakan Najeriya da suka hada da mafi akasari na kudu, mawakin na Jaruma wato Hamisu breaker ya shiga sahun mawaka na gaba gaba da aka fi jin wakokinsu a wannan shekarar ta 2021.
Sannan kuma Alkaluman sun nuna mawakin a saman mawakan kudu irinsu Joe Boy, Patoranking, Yemi Alade, Tekno, Kizz Daniel da sauransu.
Bayan haka Mawaki Davido ne a saman teburin sai Omah Lay a matsayi na biyu sai Wizkid a matsayi na uku.