Babu wanda ya isa ya kamani akan Fim din Makaranta wanda ake kiya jima’i, cewar Daraktan shirin Aminu Umar mukhtar
Hukumar tace Fina-Finan Hausa tana neman Aminu Umar Mukhtar ne ruwa a jallo. inda take zargin sa da Ialata tarbiyya da kuma rashin bin ka’ida yayin fitar da tallan fim din Makaranta ya nuna abunuwan da dama wanda mutane suke ganin basu dace ba.
fim a kansu ba, wadanda suka hada da madigo da batsa da makamatansu. Hakan ne ya sa shugaban hukumar tace fina-finan ta Kano, Isma’ila Na’abba Afakallah, ya shaida wa BBC cewa.
sun aika wa daraktan takardar gayyata a watan jiya domin ya je gabansu ya yi musu bayani na dalilan da suka sa
ya soma tallan fim din ba tare da samun izininsu be.
A cewarsa, Aminu Umar Mukhtar ya shaida musu cewa zai zo gabansu idan aka shiga sabuwar shekara amma bai je ba, lamarin da ya 53 suka soma nemansa ruwa a jallo.
Afakallah ya kara da cewa za su tuhumi daraktan fim din bisa laifukan da suke ganin ya aikata, Ba don mutanen Kano na yi fim din ba.
Sai dai a tattaunawarsa da BBC Hausa, Aminu ya kare kansa bisa fitar da tallan fim din, yana mai cewa bai damu da neman da hukumar tace fina-finan Kano ke yi masa ba.
Na samu labarin cewa hukumar tace fina-finan Kano tana nema na. Ban yi ko gezau ba domin kuwa ban aikata wani laifi ba in ji shi.
Fim din da na yi ba a kan mutanen Kano ko Hausawa na yi ba, na yi amfani da harsuna 17 a cikinsa. Kuma ba a Kano aka dauki fim din ba, don haka ban san dalilin da ya sa ya zama abin ce-ce-ku-ce ba.
Fim dina ba kawai yana magana ba ne game da ilimin jima’i ba, yana kuma nuna illolin kaciyar mata da wayar da kai kan abubuwan da ke faruwa a tsakanin Hausawa da ma wasu al’ummomi.
Daraktan fim din na ‘Makaranta’ ya musanta cewa wasu ne suke daukar nauyin sa domin ya bata tarbiyyar mutane, Aminu Umar Mukhtar ya ce bai yi ko gezau ba game da barazanar hukumar tace fina-finan jihar Kano.
Bidiyon tallan fim din mai tsawon minti biyu da dakika 20 da ke ta wadari a shafukan sada zumunta, ya ja hankalin mutane ne saboda yadda aka yi amfani da kalmomi irin su ‘jima’i’ da ‘bireziya’ (rigar mama) da ‘pant’ (kamfai).
A wani bangare na tallan fim din, an nuna wata matashiya tana gaya wa wata kawarta cewa tana dauke da cikin wata uku yayin da kawar tata take gaya mata cewa za ta taimaka mata domin zubar da shi.
A gefe guda kuma, an nuna wani wuri da ake cashewa tsakanin maza da mata inda suke tika rawa tare.