Labaran Kannywood
Naziru Sarkin waka yayi martani ga Mutanen da suke zagin sa sabida yana wasa da $Daloli shi da iyalin sa

A niya ne Mawaki Nazir M Ahmad wanda aka fi sani da sarkin waka ya wallafa wata bidiyon da yake wasa da $Daloli kamar Naira tare da ‘Yayan sa.
Nan take bidiyon ta janyo masa cece-kuce duba da yadda aka gan shi yana wasa da $Dalolin shi da Matar sa da kuma ‘Yayan sa.
Jama’a sun maganganu da dama akan wannan bidiyo da Sarkin waka ya wallafa a shagukan sada zumunta, wanda yawan maganar da Jama’a suke tasa ya goge bidiyon sannan kuma ya wallafa wani rubutu.
Sarkin waka yayi runutun nasa kamar haka yana mai cewa’ “Ba a fariya da chicken change.”.
Sannan kuma sai ya sake wallafa wani dan gajeren rubutu kamar haka, “Kaidai Allah ya tsareka da wawa ya yankema hukunci!”.