Advertising
Advertising
Labarai

Ina mai baku hakuri kan wahalar man fetur da wutar lantarki, sako daga shugaba Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nuna
damuwa a kan halin da yan kasa suka shiga
sakamakon karancin man fetur da dangogin
sa da kuma wutar lantarki, inda ya bada hakuri game da yanayin da ake ciki.

Advertising

Buhari ya bada hakurin ne a sanarwar da kakakin sa Garba Shehu ya fitar a jiya Laraba, Buhari yace matsalar man fetur da dangogin
sa, matsala ce da gwamnatin sa ta magance
tsawon shekaru bakwai a kasar nan.

Sai dai kuma Shugaban ya tabbatar da cewa, nan ba da dadewa ba wannan matsala ta man fetur da wutar lantarki zata zama tarihi.

Sannan ya kara da cewa, gwamnatin mu nada masaniyar cewa karancin man fetur da dangogin sa da wutar lantarki ya haifar da nakasu a kan rayuwar ‘yan kasa da kasuwanci, amma kuma sauki na nan tafe.

Advertising

Inda shugaba Muhammad Buhari yake cewa, ina mai baiwa kowa da ko ina a kasar nan hakuri.

Gwamnati na aiki dare da rana domin magance wannan matsala, an Fara gudanar da kundin gyaran matsalar man fetur din kuma muna fatan za’a samu nasara.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button