Labarai

‘Yan Sanda sunyi nasarar kama barawon da yake kashe ‘yan adaidaita sahu yana awon gaba da adaidaitar

‘YAN SANDA SUN KAMA BABBAN BARAWO
MAI KASHE MUTANE.

Sunansa Samson Eze yana da shekaru 31 yana da zama a anguwar Kampala Rukuba road cikin birnin Jos.

Yana yaudaran masu keke-napep zuwa wani
sabon gidansa da ya gina a Agingi dake Rukuba road, idan ya kaisu gidansa sai ya hallakasu ya kuma rike keke-napep din ya zama nasa.

Bayan ya kashe masu keke-napep din sai ya jefa gawarsu a cikin shaddar gidansa da ya tona, daga karshe jami’an ‘yan sandan jihar Pilato sun samu nasaran kamashi.

Masu sana’ar keke-napep ku kula sosai, ba kowani lungu zaku dinga shiga ku kadai ba, musamman barayi irin wannan suna duba kananun yara da suke tukin Kekenapep wanda sunfi karfinsu zasu iya murdesu idan sun shiga da su lungu.

Muna fatan Allah Ya tsare, Allah ya cigaba da tona asirin miyagun mutane irin Samson Eze.

Related Articles

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button