Gwamna Abdullahu Umar Ganduje ya bawa Mustapha Nabraska da Khalid mukami tare da yin Dinner ta alfarma
Gwamna Abdullahu Umar Ganduje ya bawa Mustapha Nabraska da Khalid mukami tare da yin Dinner ta alfarma
Ficaccan Darkta kuma jarumi a masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood “Falalu a Dorayi”, ya wallafa labarin wani abin farin ciki da gwaman jihar Kano Abdullahi Umar Gabduje ya yiwa jarumi Mustapha Nabraska da Khalid.
Ga abin da ya wallafa a shafin na sa na sada zumun ta instagram.
Muna godiya da Wannan Mukamai guda biyu.
1. Senior special Assistant Kannywood (Malam “Khalid Musa”
2. Special Adviser on propaganda to the Governor “Mustapha Badamasi Nabursaka“.
Jiya Bayan kammala dinner da Governor Dr. Abdullhi Umar Ganduje. Ya mika mukamai biyu ga ‘Yan uwanmu.
Daga Yau duk wani mai bukata ko matsala Tsakanin Kannywood da gwamnati to ya nemi wadanda mutum 2.
Allah ya tayaku riko, ya baku ikon gamawa cikin amana da alkairi.
Wannan ita ce wallafar da Falalu a Dorayi ya yi a shafin sa na sada zumun ta istagram akan mukamin da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yiwa Mustapha Nabraska da kuma Khalid.
Bayan wannan kuma Falalu a Darayi ya sake yin wata wallafar bidiyo tare da wani rubutu akan Dinner da suka yi tare da gwamna Abdullahi Umar Ganduje, inda yake cewa.
Alhamdulillah yanzu kenan bayan kammala Dinner tare da gwamnan jihar Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje OFR.
Wadda gwamnatin jihar kano ta shiryawa zababbun shugabannin Mation picture practitionners Assocuation of Nigeria Moppan, da kuma sauran shugabannin jihohi.