An jefe wani mutumi tare da wata mata a bainar jama’a bayan an kama su da laifin aikata zina
Wani mutumi da aka kama tare da wata mata suna zina a Arewa maso gabashin lardin Badakhshan da ke Afghanistan, an jefe su kamar yadda shar’ar musulinci ta tanadar.
Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito cewa, wani jami’i ya shaida cewa an jefe mutumin tare da matar a wata kotun shar’ar musulinci.
Kamar yadda kuka sani addinin musulinci ya haramta mace da namiji su yi tarayya da juna wato jima’i idan har ba ma’aurata ba ne.
Hakazalika idan namiji mai aure ya yi zina da matar aure kuma a ka samu shaidu guda hudu, to hukuncin su shine a jefe su har sai sun mutu.
Sannan Jami’in ya kara da cewa, mutumin da aka kama tare da matar sun amsa laifin su kuma sun ce wajen sau biyu zuwa uku suna saduwa da juna.
Wata jarida ta kasar mai suna “Hasht-e Subh” ta bayyana cewa, an jefe mutumin ne tare da matar a ranar Litinin a bainar jama’a a lardin Nasi, inda aka ce wani kwamandan Taliban ne ya bada umarnin jefe mutumin tare da matar.