Labaran Kannywood

Bayan na auri Adam A Zango na fuskanci kalubalen koma baya a harkar fim, cewar Amina Uba Hassan

Bayan na auri Adam A Zango na fuskanci kalubalen koma baya a harkar fim, cewar Amina Uba Hassan

Kamar yadda kuka sani tsohuwar jarumar masana’antar kannywood Amina Uba Hassan wacce tayi sharafin ta a shekarun baya da suka gabata, ta auri jarumi Adam a zango wanda daga baya Allah ya kawo rabuwar su.

To a wannan lokacin ne tsohuwar jarumar takw bayyana wani koma baya data fuskanta game da harkar fim tun bayan data auri jarumi Adam a zango, Amina Uba Hassan ta bayyana hakan ne a shirar da suka yi da Aminiya inda take cewa.

Bayan na zama tsohuwar matar Adam a zango zan iya cewa daga farko ya janyomin koma baya Sabida wasu furodusoshi da sauran su suna ganin suna mutunci da shi domin suna tare da shi, suna ganin kamar idan suka sa ni a fim zai iya kawo musu matsala da shi da sauran su.

Amma ni dai abinda na sani shi ne ina so in nemawa kaina suna ba wai sai don Adam a zango ba, sabida ina da abubuwa da yawa da zan ba industiri na san akwai abubuwan da zan iya yi.

Sannan bayan wannan maganar da tayi ta kara bayyana yadda ta tsinci kan ta a harkar fim inda take cewa.

Bayan na gama makarantar sakandare Allah ya ji kan Ahmed S. Nuhu wanda kanine a jarumi Ali Nuhu to a Iokacin na san shi da shi na fara haduwa har muka yi dan wani flm, sai abin yazo daidai da lokacin da zan yi aure sai kuma ba’a saki fim din ba sanadiyyar zan auri dan flm wato Adam a zango.

Amma bayan nan ban wani nuna ra’ayin fim ba sai daga baya a hankali a hankali na fara jin ra’ayin ina so in koma harkar flm.

Wannan ita ce tattaunawar da Aminiya suka yi da tsohuwar matar jarumi Adam a zango kuma tsohuwar jaruma a masana’antar kannywood wato Amina Uba Hassan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button