Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Ya’yan Sarki kano zasu kasheni ku temaka min cewar Tsohuwar jaruma Kannywood.

A lokacin da ta ke fitacciyar jaruma a masana’antar finafinai ta Kannywood, sunan ta Maijidda Ibrahim, yanzu kuma Hajiya Hauwa Bello Ado Bayero.

Advertising

Tana ɗaya daga cikin ɗimbin mata ‘yan fim da su ka yi aure kuma su na zaune a gidan miji. Tsawon shekaru 21 kenan tun da tsohuwar jarumar, wadda aka fi sani da sunan Maijidda Khusufi saboda wani fitaccen fim na Ali Nuhu da ta taɓa yi, ta ke zaune a gidan mijin ta mai suna Alhaji Bello Ado Bayero, wanda shi ne Ɗandarman Kano a yanzu, kuma ɗaya daga cikin ‘ya’yan Mai Martaba Sarkin Kano, marigayi Alhaji Ado Bayero.

Allah ya albarkaci auren nasu da ‘ya’ya shida, mata biyu da maza huɗu. Sai dai kuma kash! ashe dai ganin kitse ake wa rogo. Masu sha’awar cewa Hauwa Bello Ado Bayero na kwance a cikin daula ba su san cewa kamar a kan ƙaya ta ke zaune ba saboda wani mugun yanayi da ta samu kan ta a ciki a tsawon shekaru aƙalla 15.

Yanayi ne wanda ta daɗe ta na ɓoyewa har zuwa yanzu da ta ga uwar bari ta yanke shawarar ta sanar da duniya irin halin ha’ula’in da ita da ‘ya’yan ta su ke ciki domin gudun abin da ka je ya dawo, wato kada sai ita ko mijin ta wani ya ƙaura wata ƙurar ta tashi, a riƙa cewa to me ya sa ba ta faɗa ba tun tuni?

Advertising

Hajiya Hauwa dai ta kasance cikin wannan ƙangi mai hana barci ne ba domin komai ba sai saboda wai ita ‘yar fim ce a da, sannan kuma ba ta da kowa a dangin ta wanda ya isa ya ƙwatar mata ‘yancin ta. Shin me ya faru?

Tsohuwar jarumar ta tattauna da mujallar Fim (da izinin mijin ta) a ranar Laraba, 11 ga Mayu, 2022 saboda a kai mata agajin gaggawa ita da yaran ta. Ga yadda zantawar su da wakilin mu na Kano, Mukhta, ta kasance:

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button