Labaran Kannywood
Yanzu-yanzu: Kotu ta sallami Sadiya Haruna daga gidan gyaran hali kan kazafin da tayiwa jarumi Isah A Isah
Kamar yadda kuka sani a kwanakin nan ne wata kotu a jihar Kano ya yankewa Sadiya Haruna hukuncin zaman wata shida a gidan gyaran hali, kan wasu munanan kalamai data alakanta akan Isah A Isah jarumin kannywood.
Wanda bayan kalaman data fada akan sa ya mika ta ga hukuma inda aka yanke mata wannan hukuncin na zaman wata shida a gidan gyaran hali.
To a yau kuma munga Sadiya Haruna ta wallafa wata bidiyo a shafinta na sada zumunta instagram, inda hakan yake nuna cewa kotun ta sake ta bisa kan laifin data aikata.
zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji maganganun da Sadiya Haruna take fada bayan dawowarta daga gidan gyaran hali.
Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.