Harin jiragen yakin Sojin Nageriya ya yi sanadiyar mutuwar shugaban ISWAP Sani Shuwaram
Harin jiragen yakin Sojin Nageriya ya yi sanadiyar mutuwar shugaban ISWAP Sani Shuwaram
A labarin da muka samu daga shafin Daily Nigwrian Hausa sun ruwaito cewa: Wani harin jiragen sama da Rundunar sojin Nijeriya ya yi sanadiyyar mutuwar Shugaban Kungiyar ISWAP “Sani Shuwaram” da sauran mayakan sa a yankin Marte, in ji rahoton jaridar PRNigeria.
Kamar yadda rahoton yace, jiragen yakin masu suna Super Tucano da sauran jiragen Rundunar
Sojin Sama “NAF” sune suka yi wa sansanin
Shuwaram din luguden wuta.
Rahoton ya kara da cewa, Shuwaram ya rasu ne bisa harin bindiga da jiragen yakin suka rika zubo wa, inda ya sami muggan raunuka har su kai sanadiyyar mutuwarsa a Sabon Tumbuns da ke Tafkin Chadi.
Haka zalika wasu majiyoyi na tsaro sun tabbatar da harin da yayi sanadiyar kisan Shuwaram din, PRNigeria ta biyo cewa tuni kungiyar ta ISWAP ta nada sabon shugaba mai suna Bako George domin ya gaji Shuwaram.