Zazzafan martanin Isah A Isah ga Sadiya Haruna bayan kotu ta yanke mata hukuncin wata 6 a gidan yari
Zazzafan martanin Isah A Isah ga Sadiya Haruna bayan kotu ta yanke mata hukuncin wata 6 a gidan yari
Kamar yadda a jiya muka kawo muku labarin yadda wata kotu a jihar Kano ta yankewa Sadiya Hatuna mai kayan mata hukuncin zama a gidan yari na tsawon wata shida, dalilin fadar wasu kalamai marasa dadi da tayi akan jarumin masana’antar kannywood Isah A Isah.
Bayan wannan hukuncin da kotu da yankewa Sadiya Haruna akan kalaman da ta fadawa jarumin na cewa yana neman maza wato Luwadi da kuma kalwanci, to a yau kuma jarumi Isah A Isah fadi wata magana a cikin wata sautin murya wanda shafin VOA Hausa suka wallafa a shafin su na dandalin Facebook.
Jaridar VOA Hausa ta tattauna da jarumi Isah A Isah akan wannan hukuncin da kotu ta yankewa Sadiya Haruna, Isah A Isah ya bayyana cewa.
Abinda yasa ya kai wannan al’amarin kotu domin ta nema masa hakkinsa bisa bata mishi suna da kazafin neman maza ma’ana luwadi, kalwanci auren mutu’ah da makamantansu wanda Sadiya Haruna ta alakanta shi da wannan munanan aiyukan.
Bayan haka jarumi Isah A Isah ya kara da cewa, abinda ya hada shi da Sadiya Haruna shi ne tazo wajen sa domin ya taimaketa a harka fim daga nan har ya nuna bayason tana abubuwan da take a social media domin addinin musulunci bai yarda da su ba.
Ta dalilin hakane har taje wajen hafiz abdallah domin ya sanya ta a cikin ayyukansa na yabon manzon Allah s.a. w.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekken bayani daga bakin jarumi Isah A Isah akan abin da ya hadasu da Sadiya Haruna har ya kaita kara kotu, domin a nema masa hakkin sa kan munanan kalaman da ta hada a kan sa.