Labaran Kannywood
Martanin Tijjani Asase kan masu bayyana duniya abin da suke baiwa Ladin Cima a harkar fim
Kamar yadda kuka sani dai a yanzu ana tsaka da cece-kuce akan maganar da jarumar kannywood Ladin Cima ta fada kan kudin da ake sallamar ta a harkar fim, inda dake cewa bai fi naira dunu biyu ko uku ake bata ba.
Wannan maganar da Ladin Cima ta fada a yanzu haka ta janyo cece-kuce wanda har ta kai ga Nzir Sarkin waka ya fadi wata magana da ta sake dagula al’amarin.
To a yanzu ma ficaccan jarumi kuma Daraktan fim din Aduniya wato Tijjani Abdaullahi Asase, ya bayyana a cikin wata bidiyo inda yake tofa albarkacin bakin kan abin da yake faruwa, har ma yake ganin bai kamata a yiwa Ladin Cima haka ba game da bayyana wa duniya abin da ake bata ba.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin domin kuji cikekken bayani daga bakin Tijjani Abdullahi Asase.