Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Nafisa Abdullahi tayi martani akan maganar da Naziru Sarkin waka ya jefi ‘yan kannywood da ita

Nafisa Abdullahi tayi martani akan maganar da Naziru Sarkin waka ya jefi 'yan kannywood da ita

Har yanzu dai wasu daga cikin jaruman masana’antar kannywood suna maidawa da Naziru Sarkin waka martani akan maganar da ya fada aka su na cewa, yawancin matan fim sai anyi lalata da su sannan ake saka su a harkar.

Advertising

Wannan maganar da Naziru Sarkin waka ya fada ta biyo baya ne a lokacin da BBC Hausa ta yi shira da jaruma Ladin Cima, inda a lokacin ta bayyana cewa tun da take harkar fim ba’a taba sallamar ta sama da dubu biyu ko uku ko biyar ba.

Wanda nan take wasu Daraktoti na masana’antar suka fara tofa albarkacin bakin su kan cewa maganar da Ladin Cima ta fada ba gaskiya bane, inda suka fadi kudin da suke bata a duk sanda aka shirya fim da ita.

Bayan nan ne sai mawaki Naziru shima ya wallafa bidiyo a shafin sa na sada zumunta instagram yana mai fadin cewa, maganar da Ladin Cima ta fada gaskiya ne domin wasu ma idan za’a sanya su a shirin fim sai sun bada kudi, har ma yake cews wasu sai anyi lalata da su.

Advertising

To a yanzu kuma Ficacciyar jarumar ta kannywood Nafisa Abdullahi ta wallafa wani rubutu a shafin na sada zumunta instagram, inda take nuna bata ji dadin abin da Naziru Sarkin waka ya fada ba, inda take cewa.

A ko wane profession akwai matsaloli daban daban da mutane ke fuskanta, akwai Masu cuta, akwai Kuma wanda ake cutarwa, zantuttukan da Naziru Ahmad yayi Serious allegations ne da ba’a daukan su da sanyi ko ah ina ne.

Ah ciki har da ‘Sexual Assault’ wanda shine dalilin da ya sa na saka Kaina ah cikin abinda bai shafe ni ba, amma Kuma idan akayi la’akari da abinda ya fada ya shafe ni tunda mace ce ni.

Idan abinda yake fada Gaskiya ne Kuma yana da
hujjoji da Kuma shaidu ina cikin mutanen da suke so su san su waye masu yin hakan tunda ya fadawa duniya cewa, ga abinda ake yi toh karshen adalci wa Wanda aka zalunta shine mu san su waye Kuma mu dauki Mataki akan su.

Dan a cikin Laws din mu na kasar nan da Kuma film industry din babu inda it’s acceptable to say a lady should sleep with you for films, there are consequences and the people who’re guilty should be seriously punished.

Daga Karshe Kuma duk macen data san an taba ce Mata to give herself for films fight for your rights and tell us su waye, because if you don’t speak up baza ah taba samun gyara ba.

Wannan ita ce maganar da jaruma Nafisa Abdullahi ta fada bayan Naziru Sarkin waka ya jefi ‘yan kannywood da wannan maganar.

https://www.instagram.com/p/CZ4avMuoW8V/?utm_medium=copy_link

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button