Advertising
Advertising
Labarai

Jiragen yakin kasar Nageriya sun hallaka ‘yan kungiyar ISWAP guda 34 a harin da aka kai musu a Marte

Jirafen yakin kasar Nageriya sun hallaka 'yan kungiyar ISWAP guda 34 a harin da aka kai musu a Marte

A kalla dai ‘yan kungiyar ta’addaci ta ISWAP talayin da hudu ne 34 suka rasa rayukan su a garin Marte dake jihar Borno a wani harin bama-bamai da sojojin Najeriya suka kai ta sama, kamar yadda jaridar PRNigeria ra ruwaito.

Advertising

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da sojoji tara na rundunar sojojin Kasa suka samu munanan raunuka lokacin da ayarin motocinsu suka yi taho mu gama da wasu nakiyoyi da ‘yan ta’adda suka binne a garin Malam Fatori dake karkashin karamar hukumar Abadam ta jihar Borno, a rahoton da Daily Nigerian ta bayyana

Sannan an bayyana cewa, sojojin na shirin kai hari ne kan wasu mayakan kungiyar ISWAP dake taruwa a Tumbun Dan Katsina.

Bayan haka kuma an sami rahoto da yake kara bayyana cewa, Rundunar sojin saman Najeriya NAF tare da dakarun hadin gwiwa na kasa da kasa wato “MNJTF” a ranar Laraba, sun aiwatar da wasu hare-hare ta sama a sansanonin kungiyar ISWAP a ranar Laraba a Sabon Tumbu, wani yanki mai fadama a karamar hukumar Marte da ke jihar Borno.

Advertising

Wata majiyar sirri tace, harin na hadin gwiwa da dakarun soji suka kaddamar ya biyo bayan wani rahoto ne dake nuni da cewa an ga ‘yan ta’addar kungiyar ISWAP sama da guda dari 100 a cikin jirgin ruwan kwale-kwale masu amfani da inji a Sabon Tumbu.

A yayin da majiyar take zantawa da PRNigerian ta tabbatar da cewa, jiragen Super Tucano da aka tura cikin gaggawa domin gudanar da aikin, sun kai farmaki maboyar ‘ya ta’addan inda su ka kashe da dama daga cikinsu.

Ya kara da cewa, harin da aka gudanar a yankin gaba daya ya nuna cewa, an hangi ‘yan ta’addan sun buye a waje guda domin tsere wa daga harin da sojoji suka kai.

Sannan ya kara da cewa, cigaba da kai hare-hare ta sama ya yi tasiri a kan yaki da rundunar mayakan jihadi, tare da dakile shirinsu na kai wasu manyan hare-hare a sansanonin soji a kewayen Malam Fatori, Damasak, Gubio da Kauwa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button