Advertising
Advertising
Labarai

Sojojin sama sun yi luguden wuta ga wasu ‘yan ta’adda inda suka hallaka babban dan ta’adda Dogo Umaru

Sojojin sama sun yi luguden wuta ga wasu 'yan ta'adda inda suka hallaka babban dan ta'adda Dogo Umaru

Rundunar Sojojin Nageriya ta “NAF” tayi lugudan wuta a jiragen sama ga wasu ‘yan ta’adda inda suka hallaka wani kasurgumin dan ta’adda mai suna Dogo Umaru, wanda yake karbar umarni daga wajan shahararran dan ta’addan nan Bello Turji.

Advertising

Harin da Sojojin suka kai a jiragen saman sun hallaka wasu ‘yan ta’adda wanda a kalla zasu kai kimanin arba’in 40, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Rundunar Sojin ta bada umarnin kai wa harin ta sama bayan an tabbatar da cewa, dan ta’adda Dogo Umaru da tawagar sa ne suka shirya kai wa hare-hare da aka kai kauyen Magama dake karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.

A wani hari da ‘yam ta’addan suka kai a kwanan nan ya yi sanadiyyar rasuwa wani babban jami’in ‘yan sanda na caji ofis din kauyen Magama, sannan kuma wani Soja ya sami rauni a yayim kai wa harin.

Advertising

Inda aka tabbatar da cewa, dan ta’adda Dogo Umaru ne tare da mayakan sa suka kai wadannan hare-haren a kauyukan da suka kewaye yankin, inda suka kai harin nasu wata makarantar Firamare dake Tsambaen Dantambara wanda makarantar da dade babu mutane a cikin ta.

Sai dai kuma RP Nigerian ta sami wani labari daga wani jami’in leken asiri na Soji cewa, an tura wasu jiragen yaki guda biyu domin a hallaka ‘yan ta’addan da suke addabar al’ummar Katsina.

Kamar yadda yace, daya daga cikjn jiragen yakin ya yi luguden wutar ga ‘yan ta’addan, yayin da sauran jiragen suka bi sauran ‘yan ta’addan da suka tsere.

Majiyoyin yankin dake kusa da kauyen Tsamben Babare sun tabbatar da cewa, an hallaka ‘yan ta’adda guda arba’in da biyu 42 a harin da sojojin saman NAF suka kai musu, inda su ka ce ciki har da dan ta’adda Dogo Umaru.

Wani jami’in leken asiri na rundunar sojin Najeriya yace, dakarun soji da na sauran jami’an tsaro sun kara kaimi a rundunoni daban-daban a yankin Arewa maso Yamma a kwanan nan.

A makon da ya gabata ne wani harin da jirgin NAF ya kai tare da yakin da sojojin kasa suka yi a jihar Kaduna da jihar Neja, sun fatattaki ‘yan ta’adda da dama wadanda suke da makarantar horar da sojoji ta Nageriya da kuma wajan shadadi maudu.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button