Advertising
Advertising
Labarai

Gwamna Abdullahi Ganduje ya kori wasu ma’aikata 4 bayan an kama su da takardun bogi a harkar filaye

Gwamna Abdullahi Ganduje ya kori wasu ma'aikata 4 bayan an kama su da takardun bogi a harkar filaye

A wani labari da samu a yanzu daga shafin Daily Nigerian Hausa dake kan dandalin sada zumunta na Facebook, Gwamnan jihar Kano Avdullahi Umar Ganduje ya kori wasu ma’aikata guda hudu 4 bayan an kama su da laifin harkar filaye da takardar bogi.

Advertising

Kamar yadda shafin Daily Nigerian Hausa suka wallafa labarin kan cewa.

Ganduje ya kori ma’aikata 4 sakamakon
amfani da takardun bogi da harkallar filaye.

Gwamnatin jihar Kano ta kori ma’aikatan Hukumar Kula da Harkokin Filaye su hudu sakamakon sayar da filayen jama’a, amfani da takardun bogi da kuma amfani da jabun bayanai.

Advertising

Wannan na kunshe a wata sanarwa da
Kwamishinan Yacfa Labarai, Muhammad Garba ya fitar a yau Talata.

A sanarwar Garba ya bayyana cewa, ma’aikatan da aka kora sun hada da Abdulmumin Usman Magami, mai matakin albashi na 06, Abdullahi Nuhu Idris mai matakin albashi na 10, Audu Abba Aliyu mai matakin albashi na 05 da kuma Baba Audu da ke kan matakin albashi na 13.

Garba yace, an kori ma’aikatan ne bayan
rahoton da kwamitin bincike da gwamnati ta
kafa ya mika sakamakon binciken, bayan
korafe-korafe da a ka kai a kan su.

Sannan ya kara da cewa, gwamnati ta yi amfani da dokar aiki mai lamba 04406 domin ya zama
darasi ga yan baya.

Kwamishinan ya yi gargadin cewa, gwamnati
banza ta lamunci aikata laifukan da ga wajen
ma’aikatan ta ba.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button