Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Nan gaba kadan zamu shirya fim wanda yafi Labarina kyau da tsaruwa, cewar Darakta Aminu Saira

Nan gaba kadan zamu shirya fim wanda yafi Labarina kyau da tsaruwa, cewar Darakta Aminu Saira

Ficaccan Darakta a masana’antar kannywood Aminu Saira ya bayyana cewa, nan gaba zai shirya wani sabom fim wanda zai fi Labarina shahara da karbuwa a Duniya.

Advertising

Bayyanar wannan sanarwar ta biyo baya ne a lokacin da ake tafka muhawara a kafafun sada zumun kan cewa, Darakta Aminu Saira bai taba shirya wani fim kamar Labarina ba kuma bazai kara shirya wani makamancin sa ba.

Sai dai kuma a tattaunawar su da wakilin Notheflix Darakta Aminu Saira ya bayyana cewa, wannan hasahe ne kawai na mutane ko a baya ma na shirya fim din “Ga Duhu Ga Haske” wanda shi ma ya shahara.

Ya kara da cewa, kuma shi ma an yi cece-kuce a kan sa amma daga baya fina-finan da suka biyo bayan sa, sai ake ta fadin cewa sun fi shi kyauta da tsaruwa.

Advertising

Daga karshe Aminu Saira ya bayyana cewa, nan gaba kadan zasu shirya fina-finan da zasu fi Labarina kyau da tsaruwa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button