Labarai

A yanzu haka na shafawa Maza 119 cutar Kanjamau da Mata 19, cewar wata Budurwa wanda cutar ta jima a jikin tun 2016

A wani labari da muka samu a yanzu kan wata Budurwa ‘yar kasar Nageriya ta bayyana yawan Mutanen da ta sanyawa cuta mai karya garkuwar jiki, bayan ta tabbatar da ta dauke ta cutar tun tsawon shekara bakwai 7 data gabata 2016.

Budurwar ‘yar kasar Nageriya wanda take amfani da kafar sada zumunta ta Twitter a yanzu haka ta bayyana yadda ta sanyawa Mutane kimanin dari da goma sha biyar 115, da kuma Mata wanda suka ta sanya musu cutar har kusan su goma sha tara 19.

Kamar dai yadda ta wallafa labarin nata tana cewa.

Aminin dan uwana ne ya shafa min cutar a shekarar 2016 a lokacin ina ‘yar shakara 18 kacal.

Shi ne mutumin farko da na yi lalata da shi har sai da na kai shekara 20. Tun a watan Disamba, 2017 da aka min gwajin cutar gami da tabbatar da cewa na kamu da ita, na lashi takobin shafa wa sauran mutane cutar da aka shafa min, ba tare da amfani kwararon roba ba.

Kimanin maza 115 da mata 19 ne na shafa wa cutar, sannan ina cigaba da kirga. Tun daga lokacin, ban damu da mutuwa ba ko da yau ne. Menene amfanin rayuwa ta? Duk da na gama jami’a, bazan iya samun aiki ba saboda ina dauke da cutar kanjamau? Menene amfanin rayuwa ta idan sai na dogara da maza zan samu kudi? Menene amfanin rayuwa ta, idan sai na sha maganin ARV akai-akai don in rayu?.

A tunanin ku kuna da damar kira na azzaluma? Da ace kun san Ifeanyi, azzalumin abokin dan uwana, da kun san asalin siffar zalunci. Tunda babu wani banki a Najeriya dake son bani aiki, don kawai ina da cutar kanjamau, aikuwa dole in cigaba da yada cutar ga wasu.

Ta ci gaba da cewa idan namiji ko mace ko ma ‘yar madigo baza ta iya danne sha’awar ta ba, ba za ta damu ba idan ta shafa mata sama da sau dari.

Hakan abu ne mai sauki a wuri na, ga jindadi da kuma taya ni dandanar bakin cikin da nake ciki.

Ya dakile alakar mu bayan yi min alkawarin duniya da lahira. Tsabar damuwar da na shiga yasa na fadi wasu daga cikin darussa na a shekarar ta karshe a jami’a.

Hakan yasa nayi manejin gamawa da digiri mai daraja ta biyu daga baya, ni da ya kamata in kammala da digiri mai daraja ta daya. Yanzu na ma gama amma na gaza samun aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button